News

Akwai ƙwarin guiwa a Saudiyya cewa ɗanwasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, zai amince ya koma taka leda a gasar Saudi Pro League idan har yarjejeniyarsa ta kawo ƙarshe.